Wata sanarwa da Mataimaki na musamman na musamman ga gwamnan kan harkokin yada Labarai, Kelvin Ebiri, ya fitar, Yace sabbin masu bayar da shawarar zasu taka rawar gani a gwamnatin.
Sanarwar ta kara da cewa baya ga nadin sabbin masu bada shawara dubu 14 da gwamna Wike yayi, Kazalika ya amince da nadin mutane dari ukku da goma sha tara, a matsayin masu kula da ofisoshin gwamnati dake mazabun jihar, inda sanarwar ta ce nadin ya fara aiki ne nan take.
Idan ba’a manta ba a cikin watan Maris din bana ne, Gwamna Wike ya baiyana cewa gwamnati zata bawa mutanen dake son yin aiki tare dashi mukamai, la’akari da cewar ya cika dukkanin alkawuran da ya daukarwa jihar.