
Gwamna Nyesom Wike na jihar Rivers ya yi alkawarin bayar da tallafin ga yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso a jihar.
Wike ya yi wannan alkawari ne a ranar Litinin a lokacin da dan takarar jam’iyyar NNPP ya halarci bikin kaddamar da tituna a karamar hukumar Emohua ta jihar Rivers.
Wike, wanda ya gayyaci Kwankwaso wurin taron, ya bayyana shi a matsayin mutum mai rikon amana, wanda ke nufin alheri ga Najeriya, inda yace ya jawo hankalin Kwankwaso da kada ya bar PDP a farkon watan Maris amma makiya a cikin jam’iyyar sun kore shi.
Wike ya ce tsohon gwamnan na jihar Kano yana da abin da ake bukata domin tafiyar da Najeriya.
Ya kuma bukaci Kwankwason ya tuna da mutanen Rivers idan ya yi nasara.