Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, ya ce ‘yan siyasa a jihar sun fara daukar ’yan daba da tsaffin masu laifi domin a yi amfani da su a matsayin ‘yan jagaliyar siyasa kafin da kuma lokacin zabukan 2023.
Gwamnan a cikin wata sanarwa da ya fitar a jihar ya ba da rahotanni da ke nuna cewa ana gudanar da tarurrukan daukar ‘yan jagaliyar a otal-otal da sauran wuraren shakatawa na jihar.
Ya kuma yi gargadin cewa gwamnatin sa ba za ta bari duk wani dan siyasa ya tayar da zaune tsaye da hukumomin tsaro suka yi ta kokawa a jihar Rivers ba.
Sai dai ya yi gargadin daukar tsauraran matakai kan wadanda ke da hannu a wannan gagarumin shiri na aikata miyagun laifuka.