Gabanin ziyarar da shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kai jihar Imo a ranar 12 ga watan Yuli, Gwamna Hope Uzodimma ya bayar da wa'adin kwana 10 ga 'yan bindiga a jihar da su ajiye makamansu.
Uzodimma ya shawarce su da su bar dazuzzukan jihar su mika kansu ga sarakunan gargajiya domin a yi musu afuwa ba tare da wani sharadi ba.
Da yake zantawa da manema labarai a Owerri, Uzodimma ya ce jihar za ta gudanar da bikin ranar sojoji a kowace shekara daga ranar 30 ga watan Yuni zuwa 6 ga watan Yuli kuma za a gudanar da bikin zagayowar ranar sojoji da kasa da sojoji dubu 10 da aka zabo daga cikin Sojoji, Na ruwa da Sojojin Sama da ‘yan sanda da dai sauransu da zasu halarta.
Gwamnan ya ce jihar za ta kai kayan aikin soji da za a yi amfani da su wajen kawar da ragowar ‘yan bindigar da ke boye a cikin dazuka daban-daban a jihar.