Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom ya bukaci dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar da ya nemi afuwar sa bisa zargin sa da yi masa karya.
Gwamna Ortom ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin wata kungiyar matasan Jemgbagh, a yayin wata zanga-zangar da suka gudanar zuwa gidan gwamnatin jihar dake Makurdi, kan karyar da suka ce Atiku ya yi masa.
Gwamnan ya bayyana cewa ya kamata tsohon mataimakin shugaban kasar ya fito filo ya nemi afuwar gwamnan kan zargin da ya yi na cewa ‘yan uwansa na satar shanun makiyaya a jihar.
Ya soki ikirarin da Atiku ya yi na cewar, Gwamnan yayi All..h wadai da daukacin Fulani , yana mai cewa bai taba fadin haka ba.
Sai dai kuma Gwamna Ortom ya ce duk da rikicin da PDP ke fama da shi, zai yi kokarin ganin ta samu nasara a dukkan matakai a jihar.