Gwamna Samuel Ortom na jihar Benuwe ya rubutawa shugaban kasa Muhammadu Buhari wasikar neman lasisin mallakar bindigogi ga sabbin jami’an sa kai na jihar Binuwai da aka kaddamar a makon jiya.
Ortom wanda ya bayyana hakan a ranar Litinin a Makurdi, yace matakin ya zama dole ne biyo bayan halaltacciyar hanyar da akabi wajen kafa jami’an tsaron na sa kai don taimakawa wajen dawo da zaman lafiya a sassan jihar da ke fama da rikici.
Ya ci gaba da cewa yana fatan shugaban kasa zai amince da bukatarsa ta karfafawa ‘yan kasa don tabbatar da matakin kare kai.
A yayin kaddamar da jami'an a makon da ya gabata, Gwamnan ya bukaci jami'an da su guji yin amfani da karfin ikon da dokar jihar ta ba su wajen wuce makadi da rawa.