Gwamnan jihar Benue, Samule Ortom ya dakatar da gudanar da aiyukan Hukumar kula da kungiyoyin tsaro masu damara na jihar har nan da tsawon makwanni biyu masu zuwa.
Hukumar dai ita ce wadda aka dorawa alhakin tabbatar da dokar nan ta haramta yin kiwo a fili, Gwamnan ya ce matakin zai baiwa makiyaya dake da dabbobi damar ficewa daga cikin jihar.
Gwamnan ya baiyana daukar matakin nea yayin wani taro na majalisar tsaro na jihar da aka gudanar a ranar Talata, bayan da aka halaka mutane sama da 130 a cikin mako daya a jihar.
Samuel Ortom ya ce daukar matakin zai baiwa makiyayan da suka shiga jihar batare da sanin an haramta yin kiwo a fili ba, damar gaggauta ficewa daga cikin.