Gwamnatin jihar Zamfara ta umarci daukacin kungiyoyi masu zaman kansu dake aiki a jihar ba bisa doka ba, dasu gaggauta ficewa daga jihar batare da bata wani lokaci ba.
Wata sanarwa da kwamishinan tsaro na jihar, Mamman Tsafe ya fitar, ta baiyana cewa an gano wasu daga cikin kungiyoyin suna temakawa waje matsalar tsaro da jihar ke ciki da kuma makotanta.
Tsafe ya ce an umarci dukkanin hukumomi da kuma ma’aikatun gwamnati dasu yanke duk wata alaka tsakaninsu da kowace irin kungiya batare da wata jan kafa ba.
Bugu da kari ya ce za’a dauki matakin hukunta duk wata hukuma ko ma’aikata da aka samu tana hulda da irin wadannan kungiyoyi.