Kotun koli ta tabbatar da zaben Muhammad Yahaya a matsayin gwamnan jihar Gombe, inda ta yi watsi da karar da Jibrin Barde na jam’iyyar PDP ya shigar.
Kwamitin Alkalai biyar na kotun kolin karkashin jagorancin mai shari’a Kudirat Kekere-Ekun ya tabbatar da hukuncin kotun daukaka kara.