On Air Now

ZANGON RANAR ASABAR

Noon - 6:00pm

Gwamna Ganduje Ya Kori Baba Impossible Daga Matsayin Kwamishinan Addinai

Gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya tsige kwamishinan harkokin addinai, Dr. Muhammad Tahar Adam da akafisani da Baba Impossible daga mukaminsa.

Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida na jihar Kano, Malam Muhammad Garba, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, 31 ga watan Disamba, yace an sauke Baba Impossible daga mukamin ba tare da wani bata lokaci ba.
 
Yace korar kwamishinan kuma dan majalisar zartarwa ta jihar ya biyo bayan halin rashin da’a da ya nuna a matsayinsa na ma’aikacin gwamnati mai rike da mukami.

Malam Garba ya yi nuni da cewa, an kuma same shi da mayar da aikin ma'aikatar tamkar  wata  sana’a ta kashin kansa, har ma yana rage ranakun aiki ga ma’aikatan ma’aikatar, inda ya cire musu ranakun Laraba da Juma’a. 

Kwamishinan na yada Labarai, ya kara da cewa baya ga gudanar da aiki ba tare da tuntuba ba, Baba Impossible baya biyayya ga gwamnati. 

Ya kara da cewa tuni Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya aikewa majalisar dokokin jihar Kano sunan Dr Nazifi Ishaq Bichi na Jami’ar Bayero ta  Kano a matsayin wanda zai maye gurbin kwamishinan bayan tantancewa.

Sanarwar ta kara da cewa, Ganduje ya yiwa korarren kwamishinan fatan alheri.