Gwamnatin jihar Kano ce ta bada umarnin rushe wani haramtaccen gini da aka yi shi a fitaccen filin nan na sheik Nasiru Kabara dake cikin birnin kano, kamar yadda aka yi aikin rusau din a daren ranar Litinin.
Gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ne ya bada umarnin rushe ginin bayan binciken da aka gudanar ya gano cewa, babu wata amincewa ta hukuma da aka samu wajen yin ginin a filin wanda ya kasance mallakin masarautar Kano.
Wata sanarwa da Kakakin Hukumar KAROTA, Nabilusi Abubakar Kofar Na’isa ta Ambato gwamna Ganduje na bada umarnin kewaye wani bangare na wurin da Katanga domin mayar dashi wurin shakatawa da wasannin Yara, Sannan kuma wani bangaren za’a rika yin amfani dashi domin Zikirin kadiriyya.
Kazalika sanarwar ta Ambato shugaban hukumar KAROTA, Baffa Babba Dan Agundi wanda kuma shine shugaban kwamitin rushe haramattun gine-gine na musanta rahotannin dake cewa anyi rusau din ne batare da samun izini ba.