
Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i, Ya soke shaidar takardar mallakar fili ta wasu kanfanoni guda tara, mallakin tsohon gwamnan jihar Sanata Ahmed Muhammed Makarfi.
Kazalika gwamnan ya bada umarnin rushe wuraren da abun ya shafa,kamar yadda aka aike da takardar sanarwa ga ma’aikatan dake aiki a kanfanonin,jim kadan bayan da gwamnan jihar ya janye shaidar takardar mallakar fili ta kanfanonin.
Biyar daga cikin filayen suna a yankin Mogadishu sai guda ukku dake akan titin Kwato da kuma wani guda daya a yankin Doka.
Sanata Makarfi wanda ya tabbatar da daukar matakin ga manema Labarai a ranar Alhamis, Yayi alkawarin cewar lauyansa zai garzaya gaban kotu domin hana daukar matakin rushe wuraren.