Gwamnan jihar Bayelsa , Sanata Douye Diri ya zama dan takarar gwamnan jihar a karkashin jam’iyyar PDP a zaben gwamnan jihar da za’a yi ranar 11 ga watan Nuwambar bana.
An gudanar da zaben fidda gwanin ne a ranar Laraba, Kuma ba ‘a samu wanda ya tsaya neman tikitin takarar tare da gwamnan mai ci ba
Shugaban kwamitin shirya zaben wanda kuma shine gwamnan jihar Osun, Sanata Ademola Adeleke ya baiyana cewar gwamnan ya samu kuri’a 305, wanda hakan ya bashi damar zama dan takara batare da hamaiyya ba.
Shima a nasa jawabin, Gwamna Diri ya baiyana godiyarsa ga wakilan jam’iyyar saboda damar da suka sake bashi domin ganin ya sake yin tazarce akan kujerar gwamnan jihar.