
Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq ya zama shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya.
Sanarwar wani taron gaggawa da gwamnonin suka yi a daren ranar Talata, ta ce AbdulRazaq ya zama shugaban kungiyar ne bisa amincewar juna kuma gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde a yanzu shi ne mataimakin shugaba.
Sanarwar ta kuma jaddada cewa mambobin sun bayyana gamsuwarsu da nasarar kammala taron bita ga sabbin gwamnoni da masu dawowa da suka yi a makon jiya.
Gwamnonin sun kuma kuduri aniyar ci gaba da yin hadin gwiwa ta hanyar inganta kwarewa da zurfafa alaka da Gwamnatin Tarayya da sauran cibiyoyi.