On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Gwamna Abba Zai Samar Da Sana'oin Dogaro Da kai Ga Tubabbun Masu Aikata Lefi

GWAMNA ABBA

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf Ya yi alkawarin samarwa matasan da suka tuba daga aikata lefuka sana’oin dogaro da kai, domin su kasance masu tarbiya a cikin al’umma da kuma tsayawa da kafafunsu.

Gwamnan ya tabbatar da haka ne a ranar  Talata a filin  wasa na Sani Abacha, a  yayin wani horo da aka shiryawa  Tubabbun ‘yan daba  guda 222  da rundunar  yansandan jihar kano ta shirya.

Sanarwar da  kakakin gwamnan jihar Kano Sanusi Bature  ya fitar, ta Ambato gwamnan na jihar  kano na cewar akwai shiri a kasa, na koyar da matasan sana’oin dogaro da kai da kuma masu  tallafin karatu.

Ya kuma  godewa  kwamishinan yansandan jihar kano Muhammad  Usaini Gumel  saboda  horon da aka shiryawa  matasan da suka  tuba  daga aikata lefuka.