On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Gwamna Abba Ya Rage Kudin Makaranta Ga 'Dalibai 'Yan Asalin Jihar Kano A Manyan Makarantu

Gwamnatin jihar Kano ta rage kudaden manyan makarantu mallakin jihar da kashi 50 cikin 100 ga dalibai ‘yan asalin jihar.

Kwamishinan ilimi mai zurfi na jihar Dr Yusuf Kofar Mata ne ya tabbatar da hakan a daren da ya gabata.

Kofar Mata ya ce gwamnati ta dauki matakin ne duba da irin halin kunci da ake fuskanta biyobayan cire  tallafin man fetur domin rage matsalolin da iyaye ke ciki.

Ya ce rage kudin makarantar ya shafi daukacin ‘yan asalin jihar Kano daga zangon karatu na 2023/2024 makarantun da suka hada da Jami’ar Aliko Dangote dake Wudil da Jami’ar Yusuf Maitama Sule da kwalejin fasaha ta  Kano Poly, da Jami’ar Ilimi ta Sa’adatu Rimi.

Sauran sun hada da kwalejin Legal da kwalejin aikin gona ta Audu Bako dake  Danbatta da makarantar share fag eta  Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.