On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Gwamna Abba Ya Nada Sabbin Shugabannin Hukumomi Da Ma'aikatun Gwamnatin Kano 15

Gwamna  Abba Kabir Yusuf ya nada mutane 15 amatsayin shugabannin hukumomin wasu hukumomi da ma;ikatun gwamnati.

Sanarwar sanarwar nadin na dauke da sahannun  babban sakataren yada labarai na gwamnan  Sanusi Bature Dawakin Tofa.

Ya ce nadin ya fara aiki ne nan take.

Wadanda aka nada sun hada da Farfesa Aliyu Isa Aliyu, Darakta Janar na Hukumar Kididdiga ta Jihar Kano sai Kabiru Ado Zakirai shugaban hukumar kula da manyan makarantun sakandare da akafisani da gidan malamai.

Sauran sun hadar da  Hon. Alkasim Hussain Wudil, shugaban cibiyar koyar da sana’oi ta  Aliko Dangote da Farouq Abdu Sumaila, shugaban hukumar bada shawarwari da jagoranci da Alhaji Umar Shehu Minjibir, shugaban hukumar ma’aikatan Jihar Kano.

Haka kuma gwamna Abba ya CP Kabiru Muhammad Gwarzo mai ritaya amatsayin shugaban makarantar koyar da harkokin tsaro dake Gabasawa sai Dr Abdullahi Garba Ali shugaban makarantar koyar da harkokin fasaha dake Kura da Hajiya Shema’u Aliyu shugabar cibiyar koyar da harkokin saukar baki da dai sauransu.