To yanzu haka dai a hukumance, Gwamna Abba Kabir Yusuf na nan jahar Kano ya garzaya gaban kotun daukaka kara domin kalubalantar hukuncin da kotun sauraren kararrakin zaben gwamna ta yanke na sauke shi daga kan kujerarsa ta gwamnan kano.
Gwamnan ya gabatar da wasu hujjoji har guda 23 a gaban kotun daukaka karar, wanda yake fatan zata yi amfani dasu domin soke hukuncin da kotun kararrakin zaben gwamnan kano ta yanke.
Ya baiyana cewar kotun ta yi abunda ya sabawa doka, a lokacin da ta dogara da sashi na 71 da kuma 63 na dokar zabe ta kasa wajen soke kuri’u dubu 165 da 616 daga cikin kuri’un da aka zabe shi da su.
A cikin kunshin karar mai shafuka 35, da gwamnan kano da kuma jam’iyyar sa ta NNPP suka daukaka, sun bukaci kotun daukaka karar data tabbatar dashi a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan kano na ranar 18 ga watan Maris din bana.