On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Gwamantin Taraiyya Zata Samar Da Motoci Sama Da Dubu 11 domin Domin Saukaka Sufuri

MOTOCIN SAFA

A wani mataki na samun sauki a bangaren sufuri a kasar nan, Shugaban kasa Bola Tinubu na hasashen mayar da litar man gas naira 250, domin ganin ya maye gurbin Man fetir da ake amfani da shi, bayan dakatar da biyan tiriliyoyin kudi a matsayin tallafin mai da gwamnati ta yi.

Mai magana da yawun shugaban kasa Ajuri Ngelale   ya ce matakin wani bangare ne  na shirin komawa yin amfani da Gas.

Ya ce shirin wanda  ke karkashin shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila, Zai samar da  sabbin motoci dubu 11 da 500 masu amfani da Gas a nan kusa,  domin samar da tsarin sufuri  mai rahusa a dukkanin jihohin kasar nan.

Kazalika ya ce matakin zai temaka wajen kawo sauki  kan  litar man fetir da ake siya har naira  620.