
Duk da tarin sukar da ake samu daga bangaren masu ruwa da tsaki da kuma masu amfani da Kayayyaki, gwamnatin taraiyya tace ba gudu ko ja da baya kan shirinta, na kara harajin kudin kiran waya da kuma na amfani da Data da kimanin Kaso 5 bisa 100
Da zarar an fara aiki da sabon tsarin, yan Najeriya zasu rika biyan kaso 12 da digo 5 bisa 100 akan kiran waya da kuma kaso 7 da digo 5 bisa 100 .
Ta cikin wata sanarwa da Kakakin Ministar Kudi Zainab Ahmed Shamsuna, Tanko Yunusa , Yace kaso biyar bisa 100 na harajin zai rika shiga ne aljihun gwamnati.
Kazalika ministar tace sanarwar dake yawo kan harajin tuni aka aike da ita ga ministan sadarwa na kasa da sauean hukumomin da abun ya shafe.