Gwamna Chukwuma Soludo na jihar Anambra ya musanta cewar ya yi barazanar rage albashin ma’aikatan da suke kin zuwa aiki a ranar Litinin,saboda dokar zaman gida da kungiyar IPOB ke sakawa.
Idan ba’a manta gwamnan ya yi barazanar zabtare albashin ma’aikatan da basa zuwa aiki a ranar Litinin, a yayin bukin ranar ma’aikata da aka yi shekaran jiya.
Sai dai bayan sa’o’i 24 da gwamnan ya yi wannan furuci, gwamnatin jihar ta musanta barazanar rage albashin ma’aikatan da ke kauracewa aiki a ranar Litinin.
A wata sanarwa da babban sakataren yada labaran gwamnan Mister Chris Aburime, ya fitar, ya ce ba a yi wa ma’aikatan barazana ba, sai dai kawai gwamnan ya shawarce su da su daina zama a gida a ranar Litinin.