Hukumar kashe gobara ta jihar ta tabbatar da samun kiran gaggawa ta hannunn sashen karbar kiraye-kirayen gaggawa na hukumar da karfe 02:32pm na ranar laraba daga wani Muhammad Yusuf wanda ya bada rahoton tashin gobara a yankin Sardauna Crescent dake unguwar Badawa Layout karamar hukumar Nassarawa ta jihar Kano.
A cewar mai magana da yawun hukumar Saminu Yusif Abdullahi bayan samun rahoton 'yan kwana-kwana daga Sakatariyar Audu Bako da Bompai da wasu daga shalkwatar hukumar sun isa wurin da lamarin ya faru da misalin karfe 02:37pm na rana inda suka tarar gobarar ta kama a wani gini dake zama sashen injinan janareta a babban asibitin Muhammadu Buhari dake Giginyu.
Yace sun tarar da tankunan man dizal guda biyu sun kone kurmus, a kusa da wasu injina guda huɗu sun kama da wuta inda wani bangare na rufin dakin ya kama da wuta kaɗan.
Saminu yace jami'an sun samu mutum mai suna Jemoh Ajani dan kimanin shekara 40 a duniya a cikin gobarar wanda ya fita daga hayyacinsa, hakan ta sa akayi gaggawar kaishi asibitin kwararru na Muhammad Abdullahi Wasai inda daga baya aka tabbatar da rasuwarsa.
An mika gawar mai waldar ga Kofur Usaini Usaini na offishin ‘yan sanda na Badawa.
"Bisa kyakykyawan kokari na jami'anmu mun samu nasarar shawo kan lamarin tare da Kubutar da sabbin janareta guda huɗu tare da kare yaduwar wutar zuwa gidajen makwabta" Inji Saminu Yusif Abdullahi.
Ya kuma bayyana dalilin faruwar gobarar da yin waldawar tankin man diesel da ya bule.