Akalla mutum 41 ne suka mutu yayin da 45 suka jikkata sakamakon wata gobara da ta tashi a wani coci dake birnin Giza na kasar Masar, kamar yadda wasu majiyoyin tsaro suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.
Gobarar wadda hukumomi suka ce lantarki ce ta haddasa, ta tashi da misalin karfe 9 na safe agogon kasar a lokacin da ake tsaka da gudanar da ibadah, yayin da mutane 5,000 suka hallara a cocin Coptic Abu Sifin da ke yankin Imbaba, a cewar hukumomi.
Rahotanni sun ce gobarar ta toshe kofar shiga cocin, inda ta yi taho-mu-gama da wadanda suka jikkata ko kuma suka mutu, yawancin wadanda suka mutu yara ne.
“Mutane na taruwa a hawa na uku da na hudu, sai muka ga hayaki na fitowa daga bene na biyu, mutane suka ruga domin sauka daga benen, ” in ji Yasir Munir, wani mai ibada a cocin.
“Sai muka ji karar hayaniya da tartsatsin wuta suna fitowa daga tagar” in ji shi, yana mai cewa shi da ‘yarsa suna a kasa abin da ya sanya ma kenan suka iya tserewa.