kungiyar nan ta ‘Yan awaren yankin kudu maso gabashin kasar nan da aka fi sani da IPOB, ta kalubalanci shugaban kasa Muhammadu Buhari, Inda ta baiyana cewar girman zunubin da ya aikatawa ‘yan Najeriya abune da ba za’a taba yafe shi ba.
Ta cikin wata sanarwa da kakakin kungiyar Emma Powerful ya fitar, Kungiyar ta maida martani ne kan neman yafiya da shugaban kasar ya yi ga wadanda ya bata mawa saboda yanayi na gabatar da aiki, a kwanan nan.
Sanarwar da kungiyar ta Fitar, Ta ce zunubin da shugaban kasar ya aikata abune da ba za’a yafe ba,Kuma zai girbi abunda ya aikata a lokacin da ya kammala mulki.