Ambaliyar ta lalata gidaje kimanin 250 a wasu garuruwa dake cikin karamar hukumar Tangaza a jihar Sokoto.
Kakakin Hukumar Bada agajin gaggawa na jihar, Abubakar Ghani shine ya ya tabbatar da haka ta cikin wata sanarwa, yana mai cewa mutane da dama ne suka rasa muhallansu.
Ya kara da cewa abun alhinin ya faru ne a karshen mako, inda amaliyar ta shafi garuruwan da suka hada da Shiyar Ajiya da kuma Runji.
Mashawarci na musamman ga gwamnan jihar Aminu Waziri Tambuwal , Alhaji Zubairu Magaji wanda ya jagoranci tawagar gwamnati zuwa garuruwan, Yace gidaje 250 ne suka lalace a garuruwa ukku.