Kakakin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, Malam Garba Shehu, Ya ce da mai gidansa ya cire tallafin man fetir, Da shugaban kasa na yanzu, Bola Tinubu ya fadi a zaben shugaban kasa.
Idan ba’a manta ba, Shugaban kasa mai ci, a lokacin da yake jawabi ga wasu ‘yan Najeriya mazauna kasar Faransa, Ya ce rashin kwarin gwiwa ce ta sa aka ki janye tallafin man, kafin shi ya kaiga daukar matakin cire shi baki daya, a lokacin da ya gabatar da jawabi ga ‘yan kasa, jim kadan bayan shan rantsuwar kama aiki.
Sai dai a wata sanarwa da kakakin tsohon shugaban kasa, Malam Garba Shehu ya fitar a ranar Litinin, Ya kare matakin da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dauka na kin janye tallafin man fetir, domin gudun kada jam’iyyar APC ta sha kaye a zaben shugaban kasa a da aka yi ranar 25 ga watan fabarairun bana.
Garba Shehu ya ce , Kamata ya yi Tinubu ya zama dan siyasa mai gaskiya, sannan kuma ya gane cewar da an janye tallafin man, ta hanyar aiki da dokar sarrafa albarkatun man fetir, to babu shakka da jam’iyyarsu ta fadi a zaben da ya gabata.