Ana zargin Gara ta cinye wasu muhimman takardu asusun amintattu na Hukumar Inshorar Al’umma ta kasa, masu dauke da bayanan yadda aka kashe zunzurutun wasu kudade har naira bilyan 17 da milyan 100, kamar yadda jami’an hukumar suka baiyanawa majalisar dattawa.
Jami’an Hukumar sun baiyana haka ne a lokacin da suka baiyana gaban kwamitin majalisar dattawa mai kula da baitul malin gwamnati.
Bayanin hakan dama sauran wasu jawabai na kunshe ne cikin wani rahoton babban mai kididdiga na kasa da aka fitar tun a shekarar 2018.
Binciken ya biyo bayan yadda Babban Mai kididdiga na kasa ya tuhumi hukumar asusun amintattun Inshora ta kasa, kan yadda ta kashe wasu kudade tun daga shekarar 2018.