Babban lauyan gwamnati kuma kwamishinan shari’a na jihar Kano, Barrister Lawan Musa, Ya ce gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje a shirye yake ya saka hannu kan hukuncin kisa ta hanyar rataya da aka yankewa, sheik Abduljabbar Nasiru Kabara.
Wata babbar kotun shari’ar Musulunci dake zamanta a kofar Kudu, karkashin mai shari’a Ibrahim Sarki Yola ce ta yanke Abduljabbar Nasir Kabara hukuncin kisa ta hanyar rataya, a saboda yin kalaman batanci ga annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasalam.
Da yake tsokaci akan hukuncin, Kwamishinan shari’a na jihar Kano, Ya ce a kowane lokaci gwamna Ganduje na kokarin cewar ba a karya doka da oda a jihar nan ba.
Ya kara da cewa akwai matakai da dama da ake bi kafin saka hannu kan dokar hukuncin kisa, kuma gwamnan a shirye yake ya saka hannu kan hukuncin kisan, da zarar an gabatar masa dashi.
A jiya ne, Mai shari’ar bayan ya yanke masa hukuncin kisa ya kuma bada umarni rufe masallatan sa guda biyu dake filin mushe da kuma wanda ke unguwar Sabuwar Gandu a nan Kano, sa’an nan kuma gwamnati zata kai littafan sa dakin karatu na jihar Kano.