On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Ganduje Zai Rantsar Da Sabbin Kwamishinoni 11

Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, zai rantsar da sabbin kwamishinoni 11 a majalisar zartarwa ta jihar ranar laraba.

A cikin wata sanarwa daga offishin kwamishinan yada labarai Muhammad Garba, ganduje ya shirya bikin rantsar da sabbin kwamishinonin ranar Laraba 31/08/2022 a rufaffen dakin wasa na Sani Abacha dake kofar Mata, da karfe 1 na rana.

Sanarwar ta gayyaci ‘yan majalisar dokokin jihar Kano da kwamishinoni da Iyayen kasa da jamian gwamnati da shugabannin jamiyyar APC da shugabannin kananan hukumomi da ‘yan siyasa da malamai da yan kasuwa da daukacin jama'a zuwa taron bikin.

Kwamishinonin da za’a rantsar sun hadar da

1.Rt.Hon.Yau Abdullahi'Yan Shana.

2.Hon.Adamu Abdullahi Fanda.

3.Ibrahim Dan Azumi Gwarzo.

4.Lamin Sani Zawiyya

5.Abdulhalim Abdullahi Liman

6.Dr.Yusuf Jibrin Rurum

7.Alhaji Sale Kausani

8.Dr.Ali Musa Hamza Burum Burum

9.Dr.Aminu Ibrahim Tsanyawa

10.Kabir Mohammad

11.Hon.Garba Yusuf Abubakar

Haka kuma sanarwa ta bukaci  dukkanin wadanda zasu je rakiya ko kallon taro, dasu kasance cikin da'a da bin doka da oda.