Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje ya ce mataimaka a kasar nan, dole ne su kasance masu yin kamun kafa da biyayya ga Iyayen gidansu idan har suna son tsira daga fadawa cikin tarkon wasu ‘yan bani na iya da kuma kaucewa tashin ‘yan kunji-kunji nan da can.
Ganduje ya bayyana haka ne a yayin kaddamar da wani sabon littafinsa mai suna, Tafiyar da harkokin Mataimaki da kuma jagoranci a Najeriya wanda aka yi ranar Talata a Abuja.
Ya ce littafin, wanda ya bada bayanin yadda ya fahimci abubuwan da suke wakana a kasar nan, yana daya daga cikin abunda ya shafi rayuwarsa a aikin gwamnati.
A cewarsa, tarihin dangantakar da ke tsakanin wasu Gwamnoni da mataimakansu a kasar nan tun a Jamhuriyya ta farko ta kasance ta rashin aminci da hassada da kuma cin amana.
Ya ce irin wannan matsaloli su temaka wajen raba kan jihohi da dama a shekarun da suka gabata, tare da yin illa ga ci gaban mutanen da suka zabi mutanen domin jan ragamar aiyukansu na gwamnati.
Gwamnan Jihar kano Abdullahi Umar Ganduje.
To sai dai kuma a yayin da gwamna Ganduje ke bayar da shawara ga mtaimakan gwamnoni akan su kasance masu biyayya, Shi kuwa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan kira yayi da a samar da doka da zata kare mataimakan gwamnoni daga tsige su daga kan kujerunsu ba bisa ka’ida ba.
Da yake jawabi a wajen kaddamar da littafin da gwamna Ganduje ya rubuta da hannunsa, Jonathan ya ce ya kamata ka’idojin da doka ta tanada su sanya mataimakan gwamnoni su kasance masu samun cikakken tsaro domin gudanar da aiyukansu batare da wani shayi ba.
Tsohon shugaban kasar, wanda shi ne shugaban taron, ya ce kamata ya yi a samar da tsarin doka domin faiyace irin aiyukan da suka wajaba a kan wuyan mataimakan gwamnoni , a maimakon dorasu kan wasu aiyuka na wucin gadi.
A cewarsa, matakin zai rage zaman dar-dar da ake samu a bangaren harkokin gudanar da mulki.
Tsohon shugaban kasa, Good Luck Jonathan.