Gwamnatin da ta shude a jihar Kano ta bayyana wani labari amatsayin yaudara da rashin gaskiya da ke nuna cewa ta samu lamuni na Naira biliyan 10 domin samar da Kyamarorin tsaro CCTV a cikin birnin jihar.
A wata sanarwa da tsohon kwamishinan yada labarai, Muhammad Garba ya fitar, ya ce an dauki hayar wata kungiyar hadin gwiwa dake nazarin harkokin siyasa da gwamnatin domin bata sunan tsohuwar gwamnati ta hanyar Ikirari akan kudaden.
Garba ya bayyana cewa da gaske gwamnatin da ta shude ta kudiri aniyar aikin domin inganta harkar tsaro a jihar, amma wata babbar kotun tarayya da ke Kano a ranar 1 ga Yuli na 2022 ta bayar da umarnin hana gwamnati karbar lamunin.