Nan kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya yi alkawarin farfado da martabar jam’iyyar APC.
Ganduje ya baiyana haka ne a Abuja lokacin da yake karbar bakuncin wata kungiyar masu goyon bayan jam’iyyar APC ta kasa,gabanin sanar dashi a matsayin shugaban jam’iyyar na kasa a hukumance.
Kazalika ya baiyana takaicinsa dangane da Murabus din da Salihu Lukman ya yi daga kan matsayin mataimakin shugaban jam’iyyar na kasa mai kula da shiyayr Arewa maso yamma.
A cewarsa bai kamata ya sauka daga kan kujerar ba, kasancewar yana fadar ra’ayinsa ne ga jama’a, kan kalubalantar dora Gandujen a matsayin shugaban jam’iyyar na kasa.