
“Kuna da sauran wa’adi daga yanzu zuwa ranar Juma'a, 26 ga watan Mayu da muke ciki na 2023, ku mika al'amuran hukumomin ku ga manyan sakatarori ko Daraktocin mulki da kudi.
Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ne ke bada wannan umarni ga dukkan masu rike da mukaman siyasa a jiharnan gabanin rantsar da sabuwar gwamnati a ranar 29 ga watan Mayu.
Sanarwar da gwamnatin jihar ta fitar ta ce wadanda abun ya shafa sun hada da kwamishinoni da masu ba da shawara na musamman, da manyan jami’an gudanarwa na kamfanoni mallakar gwamnati da dai sauransu.
Sanarwar ta kuma ce jami’an gwamnati da aka nada a hukumomi wadanda keda dokoki kan takamaiman lokaci su ne kawai zasu cigaba da aiki.