On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Ganduje Ya Nada Manyan Sakatarori 12

Gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya nada sabbin manyan Sakatarori 12.

Mutanen da aka nada  sun hadar da, Injiniya Mansur Yakubu, Darakta a Ma’aikatar Ayyuka da  Salisu Dan Azumi  Daraktan Ma’aikatar Kananan Hukumomi da Masarautu da kuma Dr Sa’adatu Sa’idu Bala, Darakta daga Ma'aikatar Lafiya. 

Sauran sun hada da Ahmad Tijjani Abdullahi, wanda kafin sabon nadin nasa shi ne  sakataren zartaswa na hukumar kula da makarantun Kimiyya da Fasaha sai  Baba Sharu Dala, Daraktan hukumar Korafe-korafe da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano da Aliyu Yakubu Garo, Darakta daga Ma'aikatar yawon bude ido. 

Haka kuma akwai  Abbas Sanusi, wanda ya kasance daga bangaren shari’a sai Dr Tijjani Hussain,  sakataren zartaswa a  hukumar kula da kiwon lafiya a matakin farko  da Yahaya Nuhu Amasaye darakta daga ma’aikatar kananan hukumomi.


Har ila yau akwai  Aisha Abba Kailani  daga ofishin shugaban ma’aikata sai  Mustapha Madaki Huguma darakta daga hukumar kula da ilimin bai daya SUBEB  da Musa Tanko Garko, shi ma daga ofishin shugaban ma'aikata. 

Ta cikin sanarwar da sakataren yada labaransa Abba Anwar ya fitar, gwamna Ganduje ya  hori sabban manyan sakatarorin su maida hankali wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansu.

A gobe Alhamis ne za a rantsar da su a gidan gwamnatin Kano da karfe biyu na rana.