Tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya koka kan dakatar da albashin ma’aikata dubu 10 da ya dauka aiki, da gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya yi.
Tsohon gwamnan ya koka ta cikin wata sanarwa da tsohon kwamishinan yada labarai na jihar kano, Muhammad Garba ya fitar a ranar Laraba, a wani bangare na goron barka da babbar Sallah.
Ganduje ya ce dakatar da biyan albashin ma’aikatan da ya dauka aiki ya haifar da firgici a zukatan ma’aikatan kano, a lokacin da jama’a ke fadi tashin yadda zasu tsira da rayuwarsu.
Kazalika tsohon gwamnan jihar Kanon, ya nuna damuwarsa kan soke karin girma da kuma na matakin albashi da ya yiwa malaman makarantun firamare, da gwamnan kano mai ci ya yi.