Gwamna Ganduje ya godewa kwamishinonin bisa gaggarumar gudummuwar
Gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya amince da murabus din kwamishinoninsa guda 7 da suka ajiye mukamansu domin yin takarar neman mukamai daban-daban a Babban zaben 2023.
Cikin wata sanarwa da sakataren yada labaransa Abba Anwar ya fitar, Ganduje ya amince da ajiye aikin kwamishinonin da suka hadar da mataimakinsa Dr. Nasir Yusuf Gawuna, kwamishinan noma da albarkatun kasa sai Murtala Sule Garo kwamishinan kananan hukumomi da masarautu da Ibrahim Abubakar Karaye a matsayin kwamishinan al'adu da yawon bude ido.
Haka kuma akwai Mahmud Muhammad Santsi kwamishinan sufuri da gidaje sai Muntari Ishaq Yakasai kwamishinan ayyuka na musamman da Musa Ilyasu Kwankwaso kwamishinan raya karkara da birane sai kuma Kabiru Ado Lakwaya kwamishinan Matasa da wasanni.
Gwamna Ganduje ya godewa kwamishinonin bisa gaggarumar gudummuwar da suka bayar wajen ci gaban jihar Kano tare da yi musu fatan alheri a duk inda suka tsinci kansu cikin burinsu na gaba
Saboda haka, ya umarci manyan sakatarori na ma’aikatun da abin ya shafa su dauki ragamar cigaba da tafiyar da harkokin hukumomin ba tare da bata lokaci ba.
Sai dai ganduje ya umurci shugaban ma’aikatansa da sauran kwamishinonin da su ci gaba da gudanar da ayyukan ma’aikatun su.