On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Ganduje Ya Karbi Ragamar Shugabancin Jam'iyyar APC Mai Mulki A Najeriya

Kwamitin  zartaswa na jam’iyyar APC na kasa ya tabbatar da tsohon gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, a matsayin sabon shugaban jam’iyyar na ƙasa.

An zaɓi Ganduje ne a lokacin taron kwamitin gudanarwa na  jam’iyyar maimulki da aka gudanar a birnin tarayya Abuja.

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu na cikin manyan jiga-jigan jam'iyyar da suka halarci taron na ranar Alhamis.

Haka kuma kwamitin ya tabbatar da tsohon mai magana da yawun majalissar dattawa ta 9 Sanata Ajibola Basiru a matsayin sakataren jam'iyyar APC na ƙasa.

 

Da yake jawabi,  Ganduje , ya ce  zai kai gwauro ya kai mari  wajen ganin tabbatuwar  samun nasarar  jam’iyyar  a zaben gwamnonin jihohin  Imo da Kogi da kuma Bayelsa, da za’a yi ranar 11 ga watan Nuwambar  bana.

Kazalika  Ganduje  ya godewa shugaban kasa Bola Tinubu tare da alkawarin wanzar da cikakken tsarin dimukuradiyya  a cikin jam’iyyar  a lokcin jagorancinsa.

A ranar 17 ga watan Yuli da ya gabata ne tsohon shugaban jam’iyyar na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu da babban sakataren APC Sanata Iyiola Omisore suka sanar da ajiye muƙamansu.