Gwamnatin jihar Kano ta dakatar da bikin rantsar da sabbin kwamishinonin da aka shirya gudanarwa yau domin alhini kan wadanda suka makale sanadiyar rushewar bene mai hawa uku a kasuwar Beirut
Da yake jajantawa wadanda iftila'in ya shafa, gwamna a wata sanarwa da kwamishinan yada labarai Malam Muhammad Garba ya fitar, ya bayar da umarnin a kara kaimi wajen aikin ceto wadanda suka makale a cikin baraguzan ginin.
Yayin da yake bayyana damuwa akan al'amarin, ya bayar da tabbacin cewa, ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano musabbabin rugujewar ginin.
Sanarwar ta kuma jajantawa wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a ranar Litinin da ta gabata a sassa da dama na jihar Kano, inda aka yi asarar dukiya mai yawa sanadiyar mamakon ruwan sama.