Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya bukaci al’ummar Hausa-Fulani mazauna jihar Legas da su marawa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu da abokin takararsa Sanata Kashim Shettima baya a zaben shekarar 2023.
Ganduje ya bayyana haka ne a ranar Laraba, yayin wata ziyara da Shettima, da Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas, suka kai wa al’ummar Arewa mazauna Alaba Rago a yankin Ojo na jihar ta legas.
Ya ce tuni yankin arewacin kasar nan ya riga ya karbi tsarin Bola Tinubu a matsayin dan takara.
Ya kuma ba da tabbacin cewa Asiwaju zai samu kuri’u a Kano fiye da yadda kowace jiha za ta ba shi.