Tsohon gwamnan jihar Kano,Abdullahi Umar Ganduje ya bukaci babbar kotun taraiyya dake zamanta a nan Kano, Da ta hana hukumar EFCC yi masa bincike kan wani faifan bidiyo da aka ga tsohon gwamnan yana karbar Daloli daga hannun wani ‘Dan kwangila, a matsayin cin hanci.
A cikin kunshin karar da tsohon gwamnan ya shigar da hukumar EFCC, Ya nemi kotun da ta yi la’akari da karfin da kundin tsarin mulkin kasa ya baiyana, wanda ya nuna cewar hukumar ta EFCC bata da ikon binciken tsohon gwamna, kasancewar maganar tana a gaban zauren majalisar dokokin jihar Kano.
Karar wadda tsohon babban lauyan gwamnatin kano, M A Lawan ya shigar gaban kotun, Ya nemi kotun ta tilastawa hukumar EFCC janye gaiyyatar da ta yiwa shugaban hukumar ilimin bai daya da kuma daraktan kudi na hukumar tare da babban akanta na jihar kano, domin yi masu bincike kan abunda keda alaka da faifan bidiyon karbar dalar.
Lauyan Ganduje ya ce kamata ya yi hukumar ta bari a kammala shari’ar dake tsakanin tsohon gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje da kuma mawallafin jaridar Daily Nigeria Ja’afar Ja’afar dake gaban wata babbar kotun taraiyya a Abuja, kafin daukar wani mataki a kai.