Majalisar zartaswa karkashin jagorancin Gwamna Abdullahi Ganduje a jihar Kano ta amince da kafa kwamitin mika mulki mai mutane 17 da zai mika ragama ga gwamnati mai jiran gado.
Majalisar ta kuma amince da wani karamin kwamiti mai mutum 100 wanda za a zabo mambobinsa daga ma’aikatu da hukumomi daban-daban.
Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida na jihar Kano, Mallam Muhammad Garba, wanda ya yi wa manema labarai jawabi bayan kammala taron mako-mako na majalisar zartaswa, ya ce ana saran zababben gwamna Abba Yusuf zai bada wakilai uku na babban kwamitin.
Garba ya ce, babban kwamitin zai yi aiki da nufin rubutawa tare da mika rahoton mika mulki na karshe cikin makonni uku.