Yunkurin ganin Tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya zama sabon shugaban jam’iyyar APC na kasa, na cigaba da fuskantar babban kalubale, A yayin da mataimakin shugaban jam’iyyar na kasa mai kula da shiyyar Arewa maso yamma, Salihu Lukman, ya kalubalanci matakin, inda ya baiyana cewar yankin Arewa ta tsakiya ce ya kamata ta cigaba da rike kujerar shugabancin jam’iyyar, tare da yin kira ga shugaban kasa Bola Tinubu akan ya kyale kwamitin gudanarwar jam’iyyar ya zabi wanda zai gaje buzun tsohon shugaban jam’iyyar APCN na kasa, Sanata Abdullahi Adamu.
Wata majiya ta baiyana cewar Ganduje ya yi wata ganawar sirri da sakataren gwamnatin taraiyya, George Akume jiya a Abuja, A cigaba da fadi tashin da yake na ganin ya dare kan shugabancin jam’iyyar na kasa.
To sai dai yankin Arewa ta tsakiya na cigaba da matsa lamba kan cewar, inda za’a yi adalci da kamanta gaskiya, kamata ya yi kujerar ta cigaba da kasancewa a hannunsu, kasancewar it ace yankin da aka zaba domin shugabancin jam’iyyar, a babban taron jam’iyyar da aka yi a bara.