Firayim Ministan Italiya Mario Draghi ya yi murabus daga mukaminsa bayan da kawancen jam’iyyun ‘yan biyar a kasar suka janye da goyon bayansa a wata kuri'ar nuna kwarin gwiwa da aka kada.
Sai dai shugaban kasar, Sergio Mattarella ya ki amincewa da murabus din, inda ya ya buka ce shi da yayi jawabi ga majalisar dokokin kasar domin ba da cikakken bayani akan halin da siyasar kasar ke ciki.
Ana saran Mr Draghi zai je majalisar dokokin kasar a ranar Laraba mai zuwa, bisa hasashen cewa zai iya cigaba da zama akan kujerarsa, sakamakon shiga tsakanin da shugaban kasar Mattarella yayi.