On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Festus Keyamo Ya Nemi Afuwar Majalisar Dattawa

An tabbatar da tantance tsohon karamin ministan kwadago na kasa, Festus Keyamo a cikin jerin mutanen da za’a nada kan matsayin ministoci, bayan da yaso ya gamu da cikas daga bangaren ‘yan majalisar wanda suka bukaci a dakatar da tantance shi.

Majalisar  ta cigaba  da zamanta bayan da Festus Keyamo ya nemi afuwar  ‘yan majalisar.

Keyamo  ya nemi afuwar  majalisar saboda kin amsa  gaiyatar  da aka yi masa a tsohon zauren majalisar  day a gabata.

Ya kuma ce  babban bankin kasa, shi ne  ya jagoranci raba  naira bilyan 52  ga mutanen da aka  rika  baiwa naira  dubu 20 a  matsayin ma’aikatan wucin gadi,a  zamanin gwamnatin da  ta shude.