
Gabanin kidayar jama’a da gidaje, gwamnatin tarayya ta amince da wasu kwangiloli guda biyu na Naira billiyan 15.3 domin samarwa da kuma amfani da kayayyakin fasahar sadarwa da na’urorin zamani.
Mai taimakawa shugaban kasa kan harkokin yada labarai Garba Shehu, shine ya bayyana hakan ga manema labarai na fadara shugaban kasa a jiya Laraba, jim kadan bayan kammala taron majalisar zartarwa ta tarayya na wannan mako a Abuja.
Garba ya kuma bayyana cewa majalisar ta amince da kwangilar sayen kayyakin aiki ga sabuwar makarantar horas da jami’an hukumar EFCC dake yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon-kasa akan Naira billiyan 3.3..
An tsara kidayar jama'a a fadin kasarnan daga 3 zuwa 5 ga watan Mayu na 2023 da muke ciki.