Yayinda damunar bana kecigaba da kankama manoma a birnin Maiduguri na jihar Borno na shirye-shiryen gudanar da addu'o'i na musamman kan jinkirin saukar ruwan sama a jihar dake arewa maso gabashin Najeriya.
Al’amarin ya shafi manoma da galibinsu suka fito daga yankunan arewaci da tsakiyar jihar, inda suka ce suna son a hada kai ne domin neman taimakon Allah kan matsalar.
Daya daga cikin manoman mai suna Ibrahim Ali ya koka da yadda suke ganin hadari kamar za a yi ruwan sama amma bayan wani lokaci sai ayi iska mai karfi hadarin ya washe.
Majalisar masarautar Borno, tace tana goyon bayan addu’o’in.
A wata sanarwa da ta fitar, Majalisar tace ta hada kan jama’a domin gudanar da addu’o’in rokon ruwan sama na musamman da aka shirya gudanarwa a yau Litinin 17 ga watan Yuli 2023 a dandalin Ramat da ke Maiduguri babban birnin jihar ta Borno.