
Fitaccen masanin adabin turanci farfesa Wole Soyinka ya bukaci gwamnatin Najeriya ta ayyana kungiyar Fulani makiyaya ta miyatti Allah da akafi sani da MACBAN amatsayin haramtacciya.
A lokacin da yake tattaunawa da gidan talabijin na channels a daren ranar talata, Wole Soyinka ya baiyana rashin gamsuwa akan yadda gwamnatin tarayya ke shawo kan rikicin manona da makiyya a fadin Najeriya.
Daga nan ya bukaci gwamnatin tarayya ta haramta kungiyar miyetti Allah kamar yadda ta haram kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra IPOB saboda yunkurin ballewa daga yankin kudu maso Gabas daga Najeriya
Soyinka ya dage kan cewa dole ne Najeriya ta yi la'akari da tarihinta, ta yadda za ta fuskanci kalubalen tsaro.