Hukumar Kididdiga ta kasa ta bayyana cewa farashin kayan abinci kamar naman sa da shinkafa sai wake da albasa da Doya da sauransu sun karu a watan Satumbar bana.
Rahoton ya ce matsakaicin farashin tsokar naman sa mai nauyin kilo daya ya karu da kaso 28 da digo 8 daga kan naira dubu 2 da 199 da ake siyar dashi a cikin watan Satumban bara zuwa Naira dubu 2 da 816 da kobo 91 a watan Satumban bana.
A binciken da aka gudanar kan jihohin da aka fi samun tsadar naman sa, Ya nuna cewar Jihar Anambara ana siyar da kowanne kilo daya akan naira dubu 3 da 800, Yayin da jihar Kogi ta fi kowacce jiha saukin yadda ake siyar da naman akan naira dubu 1 da 845 kan kowane kilo daya.
A yankin Kudu-maso-gabashin kasar nan kuwa, an fi samun tashin farashin shinkafa a yayin da yankin arewa ta tsakiya aka fi samun saukin farashin shinkafar a cikin watan satumbar bana, kamar yadda hukumar kididdiga ta kasa NBS ta baiyana.