Masu amfani da wutar lantarki sun soki matakin kara farashin mitar Lantarki, A yayin da suka yi kira ga gwamnatin tarayya data duba halin kuncin rayuwa da ‘yan Najeriya ke ciki, tare da gaggauta janye karin kudin da aka yi.
A ranar Laraba ne, gwamnatin tarayya ta sanar da karin kudi ga Mitocin faraway daga yau din nan 6 ga watan satumba.
A halin yanzu Mita mai amfani da layi daya zata kai naira dubu 81 da 975 da kobo 16 sabanin naira dubu 58 da 661 da ake siyar da ita a baya.
Ha kazalika mita mai amfani da layi ukku zata kai naira dubu 143 da 836 da kobo 10 a maimakon naira dubu 109 da 684 da kobo 36 da ake sayar da ita a lokacin baya.
Da yake tsokaci akan karin kudin mitar da aka yi, Sakataren kungiyar masu amfani da lantarki ta kasa, Utek Obanga, ya ce karin ya biyo bayan matsin lambar da masu samar da mitar suka yi, wanda wasunsu suka yi barazanar ficewa daga tsarin, idan har farashin ya cigaba da kasancewa a yadda yake.
Sai dai y ace a halin yanzu ‘yan Najeriya na fama ne tsadar rayuwa, musamman karin farashin man fetir da Dizal da kuma na Mita da aka yi a halin yanzu.