Kungiyar kanfanoni masu harhada magunguna ta kasa ta ce an samu karuwar kudin maganguna a kasar nan da kaso 300 bisa 100.
A cewar kungiyar, Kalubalen canjin kudi da kuma tsadar kayan da ake amfani dasu wajen samar magani, sune manyan dalilan da suka haddasa tashin magunguna a kasar nan.
A hirarsa da manema Labarai,Shugaban kungiyar, Oluwatosin Jolayemi, Ya ce kanfanonin harhada magunguna na shan wahala wajen samun canjin kudin kasashen ketare.
Haka zalika shima tsohon shugaban kungiyar masu kimiyyar hada magani ta kasa, Lolu Ojo , Ya ce kayayyakin da ake amfani dasu wajen hada magani sune abunda ke haddasa tsadarsa.